Matsalar Najeriya Adu a ce mafita,,,,,,,

 







An shawarci matasa da kungiyoyi da sukace zasu gudanar da zanga zangan lumana da su dakatar da aniyar ta su nayin zanga zangan lumana domin Samar da ingancaccen zaman lafiya a fadin kasan nan.




Darectan Da awa na kungiyar Izala dake jahar Adamawa Mallam Mukhtar Dayyib ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.





Mallam Mukhtar Dayyib yace ya zama wajibi aja hankulan matasa da su sanifa bamu da wata kasa da ta wuce Najeriya saboda haka kar muyarda mu aikata abinda zai haifar mana da matsala.






Mallam Mukhtar Dayyib ya baiyana cewa idan akasan farko zanga zangan lumana ba asan katshensana, inda ma yayi misalin da kasashen irinsu Sudan, libiya, misra, da dai sauransu duk ire ire zanga zangan ne ya jefasu cikin ukuba, a cewarsa wadannan misalai ya ishemu darasi saboda haka zanga zangan bai da amfani.





Mukhtar Dayyib yace ya kamata muyiwa kammu karatun ta nitsu Kuma a daina daukan doka a hanu duk abinda ya faru a koma ga Allah madaukakin sarki Wanda haka itace mafita.




Ya Kuma kirayi malamai da sukasance masu Jan hankalin Al umma wajen maida dukkan lamura ga Allah da yin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar baki Daya.



Harwayau ya shawarci shuwagabanin da sukasance masu sanya tsaron Allah madaukakin sarki azukatansu a Koda yaushe domin a cewarsa hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin Jama a.



A karshen ya jaddada kiransa ha matsa da su janye aniyarsu na gudanar da zanga zangan lumana maimakon haka su dukufa wajen yin adu o I Wanda hakan ne zai zai Kai su ha tudun na tsira.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.