Matsalar shaye shaye an ja hankalin Al umma da sukasance masu hada Kai.

 




An ja hankalin iyaye dama masu ruwa da tsaki da su hada Kai domin yin aiki tare domin magance matsalar ta ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin Al umma musammanma matasa.




Babban Limamin Masallacin Jumma a na Barikin yan sanda dake karewa cikin garin Jimeta CSP Ahmed Suleiman ya baiyana haka a lokacinda yake gabatar da hudubarsa ma Jumma a a Masallacin.




CSP Ahmed Suleiman yace ya kamata a tashi tsaye wajen daukan dukkanin matakai da suka dace domin ganin an kawo karshen matsalar da ke ciwa Al umma tuwo a kwarya.





Acewar  Babban Limamin Allah madaukakin sarki ya haramta Sha ko cin dukkanin abinda zaisa maye ko gusar da hankali saboda haka ya kamata Al umma su nisanta kansu dayi ta ammali a abida Allah ya haramta domin samun tsira ranan gobe kiyama.





CSP Ahmed ya Kara da cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi Shima yayi hora da a kaucewa ta ammali da miyagun kwayoyi domin itace mabudi duk wata masifa saboda haka a nisanci yin shaye shaye miyagun kwayoyi dama safaransu.





Ahmed Suleiman ya Kuma Yi Adu ar Allah madaukakin sarki da ya kare kasan nan da Al ummarta ya Kuma taimakawa shuwagabanin domin su samu damar gudanar da aiyukan cigaban kasa dama Al umma baki Daya.





Ya shawarci Yan Najeriya da su maida hankali wajen yin adu o I da Kuma sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al umma.


Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.