Rundunan yan sanda à jahar Adamawa tana tsare da mutane 8 da ake zargi da fasa runbun gwamnati.
Rundunan yan sanda a jahar Adamawa yanzu haka tana tsare da mutane takwas wadanda ake zargi da fasa runbun gwamnati harma da kwashe buhunan abinci daga runbun.
An Kuma samu nasaran kama sune biyo bayan bayanain sirri da aka samu cewa akwai wasu sun kitsa zuwa runbun gwamnati domin diban abinci.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan ta baiyana cewa daga samun rahoton kitsa wannan Shirin rundunan batayi kasa a gwiwaba wajen tura Jami an tsaro zuwa wurin runbun gwamnati dake anguwar Limawa a cikin karamar hukumar yola ta arewa Wanda hakan yasa aka samu nasaran kama mutane takwas ciki harda ma aikacin hukumar agajin gaggawa ta jahar Adamawa ADSEMA dama wasu yan Banga.
Baya ga ma aikacin hukumar ta ADSEMA da aka kama akwai Yan Banga biyu da Suma suna hanu sai sauran mutane biyar da suka hada da mata mazauna anguwar Limawane dake cikin karamar hukumar yola ta arewa a jahar Adamawa.kuma sun shiga hanu ne bayan sa o i kadan da aikata laifin.
Bayan bincike da aka gudanar an gano buhunan abinci 98 da suka hada da masara, gero, dawa da dai sauransu.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya yabawa DPO Jimeta da Jami ansa bisa jajircewa da suka Yi wajen Kai dauki domin dakile masu aikata laifuka.
Kwamishinan ya Kuma shawarci Al umma da sukasance masu taimakawa Jami an tsaro da wasu bayanain sirri a Koda yaushe domin ganin an samu damar dakawa masu kwashe kayakin gwamnati birki
Harwayau kwamishinan ya tabbatarwa Al ummar jahar Adamawa dama gwamnatin jahar cewa rundunan zata kare rayuka dama kayakin jama a.
Comments
Post a Comment