Rundunan yan sanda ta gudanar da wasanni motsa Jika ga Jami anta a jahar Adamawa.

 




Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta shiga gudanar da wasanni kamar yadda Babban sifeton Yan sandan Najeriya ya bukaci gudanar da wasanni a kowace ranan laraba a wani mataki na cigaban aikyuk Jami an Yan sandan harma da kiwon lafiya a tsakanin Jami an yan sandan.






Kakakin rundunan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.



A cewar sanarwan dai an gudanar da wasanni ne a Barikin yan sanda dake karewan an Kuma gudanar da wasanni daban daban domin karawa Jami an Yan sandan kaimi wajen gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.





Kwamishinan  Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris Wanda mataimakinsa na sashin gudanar da Mulki ACP Julios ya wakilta inda ya baiyana cewa irin wadannan wasanni suna da muhimmanci domin a cewarsa zai taimaka wajen Karin lafiya dama basu damar gudanar da aiyukansu cikin kwanciyar hankali.




Rundunan yan sandan ta kudiri aniyar ganin inganta lafiya dama aiyukan Jami an Yan aandan

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE