Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta jajintawa iyalen Marigayi DPO Maiha.

 





Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris Yana Mai nuna alhininsa tare da mika ta aziyarasa ga iyalen Marigayi CSP Yusuf Adamu Wanda Allah yayiwa rasuwar a ranan lataban nan 17-7-2024. Sakamokon gajeeuwar rashin lafiya.




Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.



Sanarwan tace CSP Yusuf Adamu Babban Jami in Yan sanda dake kula da ofishin yan sanda dake karamar hukumar Maiha a jahar Adamawa, Kuma ya rasu ya bar matarsa da yara.




Kafin rasuwarsa ya rike muka daban daban baya ga DPO da yayi  a Maiha, ya rike DPO a kananan hukumomi da suka hada da Hong, Dougire, Viniklang, da dai sauransu.




Kwamishin ya Kuma Yi adu ar Allah ya jikanshi ya Kuma baiwa iyalensa jimre hakuri Rashi da sukayi.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE