Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta tura Jami anta zuwa dukkanin rundunan zabe dake fadin jahar a yayinda ake daf da fara zaben kananan hukumomi dake fadin jahar.

 




A yayinda ake daf da gudanar da zabukan shuwagabanin kananan hukumomi da kansiloli a fadin jahar Adamawa. Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace da ita da takwarorinta na hukumomin tsaro sun tura Jami ansu a dukkanin rundunan zabe dake fadin jahar domin ganin an gudanar da zabe cikin tsanaki na tare da wata matsalaba.




Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.




Sanarwan ta baiyana cewa an dauki matakin haka ne da zumar inganta tsaro da Kuma baiwa mutane kariya dama Samar da tsaro kafin dama bayan zabe a fadin jahar baki Daya.




Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya kirayi Jami an da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa kwarewa da suke dashi tare da Kiran Al umma musammanma masu kada kuri a da su baiwa hukumomin tsaro hadin Kai da Kuma Kai rahoton dukkanin abinda basu amince da suba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE