Samar da hukumar da zata kula da dabbobi abun yabawane.






 Biyo bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya Samar da hukumar da hukumar da zata kasance tana kula da dabbobi a wani mataki na kawo karshen ta kaddama a tsakanin manoma da makiyaya a fadin Najeriya.


Hakan yasa makiyaya da manoma Ke baiyana jindadinsu dangane da wannan mataki na shugaban kasa Wanda hakan zai kawo zaman lafiya a tsakanin Manoma da makiyaya.



Alhaji Bello Ardo shugaban kungiyar Sullubawa Awareness shiyar jahar Adamawa a zantawarsa da manema labarai a Yola, ya baiyana gamsuwarsa da Jin dadinsa kan wannan matakin na shugaban kasa.


Alhaji Bello yace Daman shugaban kasa ya aiyana cewa zai Samar da irin wannan hukumar saboda a kawo karshen rikici da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya a fadin Najeriya.


Bello yace Samar da  hukumar zaitaimaka kwarai wajen dakile matsalar Wanda hakan zai kawo cigaban yadda ya kamata.


Rikici a tsakanin manoma da makiyaya dai ya dade Yana ciwa gwamnati da ma Al umma tuwo a kwarya, Kuma Yana sanadiyar asaran rayuka dama dukiyoyi masu yawa.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.