Shugaban karamar hukumar yola ta arewa yayi Kiran kan hadin Kai da zaman lafiya.

 



Shugaban karamar hukumar yola ta arewa dake jahar Adamawa Barista Jibrin Ibrahim Jimeta ya tabbatar da cewa za a samu zaman lafiya a cikin karamar hukumar duk da aniyar zanga zanga da wasu ke kudirin Yi a fadin Najeriya.




Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa daga Jami ani watsa labarai shugaban karamar hukumar Ibrahim Abubakar  a wata sanarwa da ya fitar a Yola.



Shugaban karamar hukumar wato Barista Jibrin ya kirayi masu kitsa zanga zangan dama masu ruwa da tsaki da sutabbat cewa an samu zaman lafiya a karamar hukumar ta Yola ta arewa 




Sanarwan ta baiyana cewa anjiyo shugaban karamar hukumar ya baiyana haka ne a wani taron da ya gudana a sakatariyar karamar hukumar tare da kungiyoyi daban daban harma da hukumomin tsaro.




Shugaban ya Kuma baiyana cewa ba shakka doka ya bada izinin yin zanga zanga Amma Kuma bai bada damar data hankaliba saboda haka ba zai lamuce da duk wata tashin hankaliba.




Ya Kara da cewa akwai bukatar a cigaba da Samar da zaman lafiya da hadin Kai a tsakanin Al umma da ma kungiyoyin addinai a jahar Adamawa dama Najeriya baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.