Wasanni: An yabawa gwamnatin gwamna Agbu na jahar Taraba kan harkokin wasanni.

 




An yabawa gwamnatin gwamna Agbu Kefas na jahar Taraba bisa kokarinsa na bunkasa harkokin wasanni a fadin jahar.



Shugaban kwamitin harkokin wasanni  da matasa a majalisar dokokin jahar Taraba Kuma Dan majalisar Mai wakiltar Karim Lamido Ii a majalisar dokokin jahar Taraba Hon. Anas Shu aibu ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Jalingo.




Hon. Shu aibu  Wanda Dan Jam Iyar APGA ne ya yabawa gwamna kan ma mijin kokari da yake na inganta rayuwar matasa harma da bunkasa wasanni a fadin jahar.



Hon. Anas yace kasancewa gwamna Mai Sha a war wasanni ne don haka akwai bukatan maida hankali wajen bunkasa wasanni.




Hon . Shu aibu yace kasancewa wannan gwamnatin shekara Daya a kan Mulki Al umma jahar sn gani a kasa wajen bunkasa harkokin wasanni fiye da gwamnatoci da suka shude.





Yace ko a shiga gasar wasanni da jahar ta shiga a wasanni na ciki da wajen Najeriya da cigaba da wasan Olympic da ake Yi a jahar ya nuna cewa gwamna Kefas ya baiwa bangaren wasanni muhimmanci Wanda hakan zai taimaka wajen cigaban wasanni da matasa a fadin jaha.




Shu aibu ya Kuma yaba da nada Ambasado Joseph Joshua a matsayin kwamishinan wasani da matasa wannan ma cigaba ne a harkokin wasanni.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE