Yan sanda a jahar Adamawa suna tsare da wani matashi da ake zargi da kashe abokinsa.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa yanzu haka tana tsare da wani matashi da ake zargi da hallaka abokinsa Usman ta Yi masa fashin motarsa da kudinsa dubi ashirin.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Wanda ake zargin Mai Suna Yahaya Balarabe mazaunin kauyen Dage dake cikin karamar hukumar Ganye a jahar Adamawa. Shi dai Wanda ake zargin sun tafi gonan abokin nasa wato Usman domin ya tayashi feshin Magani kwatsam sai yakaiwa Usman Sara da adda a kansa Wanda hakan yayi sanadiyar mutuwarsa sai ya jefar dashi a magudanain ruwa ya Kuma dauke motarsa da kudinsa.
An samu nasaran kama Wanda ake zarginne biyo bayan rahoton da aka samu daga iyalen Marigayi inda aka gano wasu kayakinda yayi amfani da su wajen aikata laifin.
Wanda ake zargin dai ya amsa laifinsa Kuma yace lallai ya aikata haka tare da dauke motar Marigayi da kunsinsa.
Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya baiyana damuwarsa da aukuwar wannan lamari tare da yabawa ofishin Yan sandan Karamar hukumar Ganye bisa kokari da jajircewa wajen kama Wanda ake zargi.
A kokarinta na dakile aikata laifuka a fadin jahar Kwamishinan Yan sandan ya umurci mataimakinsa dake kula da sashin manyan laifuka CID da ya gudanar da bincike dangane da lamarin.
Kwamishinan ya Kuma kirayi Al ummar jahar da sukasance masu taimakawa rundunan yan sandan da duk wasu bayanai, tare da Kai rahoton duk wadanda basu amince da aiyukansuba.
Comments
Post a Comment