Zaben shuwagabanin kananan hukumomi ya gudanar cikin kwanciyar hankali a jahar Adamawa.

 




An yabawa hukumar zabe Mai zaman kanta na jahar Adamawa bisa yadda ya shirya zabe Mai inganci da akayi a dukkanin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar.



Alhaji Adamu Jingi Wanda akafi sani da Mai hange ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai Jin kadan  bayan ya kada kuri arsa a runfar zabe dake kofar Jauro a anguwar Jambutu dake cikin karamar hukumar yola ta arewa a jahar Adamawa.


Alhaji Jingi ya baiyana gamsuwarsa dangane da yadda zabe ya gudana a kananan hukumomi ya Kuma Yi fatan za a kammala zaben lafiya a fadin jahar.


Alhaji Adamu Jingi yace zabe ya gudana cikin tsanaki ba  tare da matsalaba Kuma jama a sun fito sosai domin su kada kuri arsu Wanda hakan ya nuna gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri  tayi abun Azo a yaba dama jajircewa wajen tabbatar da adalci.



Alhaji Adamu ya kirayi Al umma da sukasance masuyin hakuri da juna da Kuma baiwa gwamnati hadin Kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran aiyukan cigaban jahar dama Al ummah baki Daya.



Ya Kuma kirayi matasa da Suma su maida hankali wajen abinda zai kawo hadin Kai da cigaba domin Suma su bada tasu gudumawa wajen cigaban jaha dama kasa baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE