Zanga zangan lumana: kungiyoyin Yan kasuwa sun gudanar da taro a Yola,
A wani mataki na kaucewa shiga zanga zanga da ake Shirin gudunar WA a fadin Najeriya kungiyoyin Yan kasuwa dake jahar Adamawa sun gudanar da taro domin tattauna yadda zasu jahankalin Al umma musammanma matasa da su nisanta kansu da shiga zanga zangan.
Taron dai ya gudanar ne karkashin shugaban kungiyar Yan kasuwar Arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 Wanda akayi a dakin taron kungiyar malamai wato N U T dake Yola.
Da yake gabatar da jawabi a wurin taron Alhaji Muhammed Ibrahim 86 yace su Yan kasuwa ba a sansu da tashin hankaliba saboda haka baiga dalilinda yasa Dan kasuwa zai soka kansa cikin wannan hayaniyaba, don haka akwai bukatan maida hankali.
Alhaji Ibrahim ya Kuma kirayi daukacin membobin kungiyar Yan kasuwa a yankin Arewacin Najeriya musammanma matasa da su nisanta kansu da shiga wannan zanga zanga da ake kokarinyi. A cewarsa ba abinda zanga zangan zata haifar sai asarar da barnata dukiyoyi da dai sauransu.
Alhaji Muhammed 86 ya baiyana cewa da zaran an kitsa zanga zanga Yana shafarsu matuka saboda sune suke ajiye kayakin sayarwa iri daban daban.
Da wannan yake kira ga Yan Najeriya da sukasance masu maida lamuranau ga Allah madaukakin sarki da Kuma dukufa wajen yin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Da yake jawabi mashawarci na musamman akan harkokin tsaro ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, Wanda shinema ya wakilci gwamna a wurin taron Alhaji Ahmed Lawan yace wannan gwamnati maici karkashin gwamna Fintiri ya maida jankaline a bangaren tsaro da zaman lafiya saboda haka bazata lamunce da wannan aniyaba,
Ahmed Lawan ya Kuma yabawa kungiyoyin Yan kasuwan bisa shirya wannan taro da sukayi Wanda acewarsa hakan zaitaimaka gaya wajen zubawa yunkuein zanga zanga ruwa, saboda haka ya jinjinawa Yan kasuwa musammanma jagoranci taron Alhaji Muhammed Ibrahim 86.
Alhaji Ahmed Lawan ya Kuma tabbatarwa Yan kasuwa dama Al ummar jahar cewa gwamnatin jahar Adamawa a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin Al umma.
Barista Jibrin Jimeta shugaban karamar hukumar yola ta arewa Shima baiyana farin cikinsa yayi da shirya irin wannan taro, saboda haka Shima Yana goyon bayan Yan kasuwa na dakile wannan zanga zanga, saboda haka Yana da muhimmanci kowa ya gargadi wadanda ke karkashinsu domin takawa zanga zangan birki.
Wakilain hukumomin tsaro da suka halarci taron da suka hada da Yan sanda, civil defence da dai sauransu dukkaninsu sun nuna farin cikinsu da shirya wannan taro domin zakulo hanyoyin da za a magance matsalar, inda suka ce a kimtse suke na ganin sun baiwa Al umma kariya a kowane lokaci.
Comments
Post a Comment