Bunkasa Noma: mata hamsin sun samu tallafi kan noma daga kamfanin Dangote a jahar Adamawa.
Kamfanin Dangote dake Numan ta kaddamar da shirin tallafin Naira miliyan biyu da rabi wa mata manoma da dake ƙauyukan da ke kewaye da ita.
A jawabin shi yayin bukin kaddamar wan da ya wakana a harabar kamfanin, gwamnan jahar Adamawa Umaru Fintiri ya gode wa kamfanin da yadda ya yunkura domin saka mata cikin shirye shiryen ya na bada tallafi.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya samu wakilcin Komishiniyar Ma'aikatar harkokin mata Neido Geoffrey Kofulto yace mata suna da jajircewa da sa kai a dukkan abun da aka saka su, shi yasa kamfanin Dangote ya ba su wannan dama domin tallafa musu.
Gwamnan ya shawarci matan da suyi amfani da wannan kudin ta hanyar da aka tsara su saboda a samu sakamakon da zai kara bude kofa domin wasu ƙarin matan su ma su amfana.
Fintiri ya godewa sarakunan gargajiyan yankin da yadda suke baiwa Kamfanin goyon bayan tafiyar da ayyukan ta da ma sauran shirye shirye wa mutanen su.
A nashi jawabi, daya daga cikin manyan jagororin kamfanin Dangote dake Numan, Chinanya Sylvain ya yabawa wa komitin da ya shirya wannan shirin bada tallafin, inda yace shirin zai taimaka gurin karfafa wa mata, tare da tabbacin cewa kamfanin a koda yaushe na shirye domin tafiya tare da mata a dukkan shirye shiryen ta.
Itama a nata jawabin, shugaban sashin sadarwa na kamfanin Dangote, Ngozi Ngena tace kamfanin zai rika sa ido kan irin nasarorin da matan suke yi tare da karin tallafi domin akwai kwararru da ake da su wanda za su rika taimaka wa a duk inda suka fuskanci wani kalubale.
Haka shima manajan sashin hulda da al'umma na kamfanin, Daniel Andrew yace makasudin shirin tallafawa mata manoma da ke wadannan al'umma shine domin tafiya da su a cikin dukkan shirye shiryen kamfanin kuma su ma su taimaka gurin ci gaban al'umomin su.
A sakon su na godiya, Hama Bachama wanda ya samu wakilcin hakimin Wayam, Cif Phineas George, da wakiliyar komitin noma na masarauta Felicia Nzomisaki da ma sauran shugabannin gargajiya sun godewa kamfanin Dangote da yadda yake hidimta wa al'ummomin wannan yanki tare da bada tabbacin cewa in Allah ya yarda kamfanin ba zai yi nadamar wannan yunkuri ba.
Da tayi jawabi a madadin mata manoma da suka ci gajiyar wannan tallafi, Clara Maxwell tace za su sarrafa wannan kudin kamar yadda aka tsara, wato yin noma .
Sun kuma gode wa kamfanin Dangote da wannan tallafi kana suka yi addu'a Allah Ubangiji ya ci gaba da baiwa Kamfanin nasarorin a dukkan ayyukan ta na wannan yankin da ma sauran yankunan baki daya.
Kimanin mata hamsin ne, goma goma da ga ƙananan hukumomin Demsa, Guyuk, Lamurde, Shelleng da kuma Numan ne a ka raba wa Naira dubu hamsin hamsin.
Comments
Post a Comment