FOMWAN shiyar Jahar Adamawa ta yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa.





Kungiyar mata musulmai ta tarayya FOMWAN shiyar jahar Adamawa.  tana Mai godewa Mai girma gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta bisa na mijin kokari da suke Yi na tallafawa mata dangane da sana o I a fadin jahar Adamawa.


Hajiya Khadija Buba Wanda Kuma itace amiran Kungiyar ta FOMWAN a jahar Adamawa ta baiyana haka a lokacinda take zantawa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.


Hajiya Khadija tace gwamna Fintiri ya taka rawan ganin wajen taimakawa mata musammanma a bangaren Samar musu da sana o I dogaro da Kai Wanda Kuma hakan zaitaimaka wajen rufawa kansu asiri.


A cewarta dai gwamnan ya basu takardun da za acike domin taimakawa matan har kuda Dari inda hakan ya basu damar rarrabawa a rassansu na kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar Adamawa.


To a gaskiya ba abida za mucewa gwamna Fintiri sai godiya tare da Yi masa fatan Allah ma daukakin sarki ya bashi damar cigaba da aiyukan cigaban jahar Adamawa baki Daya.


Amira n FOMWAN ta Kuma kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance sun baiwa gwamnatin Ahmadu Umaru Fintiri hadin Kai da goyon baya a Koda yaushe domin ganin ya samu nasaran tallafawa mata dama matasa a fadin jahar ta Adamawa domin dogaro da kansu.



Harwayau Hajiya Khadija ta shawarci wadanda suka amfana da tallafin da suyi amfani da abinda suka samu ta hanyar da ta dace domin ganin sun samu nasaran bunkasa sana o insu yadda ya kamata.



Malamai Fatima Daya daga cikin Wanda ta amfana da tallafin tace ta samu wannan tallafin ne ta hanyar Amiran ta FOMWAN biyo bayan yadda amiran taga halin da take ciki Wanda bata da abinci sai tafasa amman tunda ta samu wannan taimakon harma ta fara sana ra saida shinkafa.



Saboda haka tana mutukan godiya ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ma kungiyar ta FOMWAN bisa irin wannan jajircewa da sukayi wajen tallafawa Al umma.



Itama Malamai Hassana Abdullahi tace a baya ta shiga cikin wani yanayi na muwuyacin hali Wanda saida tana tura yaranta domin suyi bara amman a yanzu kungiyar ta FOMWAN ta sanya ta cikin wadanda suka samu tallafin Kuma ta samu saboda haka yanzu ta kama sana a ba kama hanun yaro.


Hassana tace tana godewa gwamna da irin wannan taimako da yakeyi Kuma tana masa fatan Alheri da Kuma samun nasara a rayuwarsu.


Akalla mata dubu goma ne wadanda suka fito daga kananan hukumomi 21 dake fadin jahar Adamawa ne dai suka amfana da tallafin Wanda kowanensu ta samu nera dubu hamsin.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.