Gidauniyar Attarahum tayi feshin Magani Sauro a Anguwannin Runde da Doubeli.

 




Gidauniyar Attarahum ta kaddamar da fara feshin Magani sauro a anguwannin Runde da Doubeli a wani mataki na yaki da zazzabin cizon sauro a tsakanin Al umma.


Feshin dai ya gudanar ne karkashin shugaban kungiyar a karamar hukumar yola ta Arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa Mallam Abubakar Abdullahi Isa.



Da yake zantawa da manema labarai a yayin feshin shugaban Gidauniyar a karamar hukumar yola ta Arewa Mallam Abubakar Abdullahi Isa yace dalilinsu na kaddamar da feshin shine Yana Daya daga cikin aiyukansu na tallafawa Al umma domin acewarsa gidauniyar tana hanyoyin tallafawa Al umma da yawan gaske saboda haka yasa suka ga ya dace su gudanar da feshin duba da yadda ake cikin damina Wanda Kuma ake samu yawaitar sauro a tsakanin Al umma.



Yace Yana daga cikin aiyukan gidauniyar na tallafawa marayu, marassa galihu, matan da mazajensu suka rasu Kuma suka barsu da yara, harma suna taimakawa a bangaren karatu da dai sauransu.



Ya Kuma  kirayi daukacin Al umma jahar Adamawa da sukasance masu tsafcace muhalainau a Koda yaushe domin kaucewa yaduwar sauro a tsakanin Jama a.



Shima a jawabinsa Mai anguwar Runde Mallam Yusuf Buba ya baiyana farin cikinsa da Jin dadinsa dangane da wannan feshin Maganin sauro da gidauniyar Attarahum tayi musu Wanda acewarsa hakan zai taimaka musu kwarai domin Daman suna da matsalar sauro a anguwar ta Runde.



Ya shawarci sauran kungiyoyi dama Suma suyi koyi da gidauniyar ta Attarahum wajen taimakawa Al umma domin ganin an samu nasaran yakan sauro a tsakanin Al umma.



Daya daga cikin mazaunin  anguwar ta Runde AbdulHadi Ahmed ya baiyana cewa Daman iri wannan kungiyar sukeso  saboda haka suna masu farin ciki ganin yadda wannan gidauniyar ta taimaka musu musamman ma a bangaren kiwon lafiya.


Ya Kuma baiyana cewa Yana fatan kungiyar zata fadada aiyukanta zuwa fadin jahar baki Daya. Kuma a shirye suke su marawa kungiyar baya domin ganin ta cimma burinsu na taimakawa Al ummah.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE