Gwamnan jahar Adamawa ya yabawa rundunan tsaro Civil Defence.

 




Rundunan tsaro bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence dake jahar Adamawa ta karbi takardan yabo daga gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa ta Mai bashi shawara na musamman akan tsaro da zaman lafiya Hon. Ahmed Lawan.



Wannan yabon dai na zuwane bayan da rundunan NSCDC  ta taka mahimmiuar rawa wajen inganta tsaro musammanma a lokacin zanga zangan kin jinin gwamnati da akayi na kwanaki goma.




Ahmed Lawan yace rundunan batayi da wasaba na ganin an tabbatar da zaman lafiya da Kuma bin doka da oda a fadin jahar. Sama da shekaru da suka shude. Kuma rundunan ta nuna kwarewarta matuka tare da gudanar da aiyukanta tukuru domin kare rayuka dama dukiyoyin Al umma 



Zanga zanga da aka gudanar ya haifar da kalubalen tsaro a fadin Najeriya duba da yadda ya yadu zuwa wasu sassa bisa bukatar kyakkawar gwamnati da Kuma adalci amman a jahar Adamawa ba asamu matsalaba saboda irin rawanda rundunan tsaro NSCDC ta taka wajen inganta tsaro.



A jawabinsa Kwamandan Rundunan a jahar Adamawa Ibrahim Mainasara ya baiyana farin cikinsa da Jin dadinsa ga gwamna bisa yadda ya amince da Kuma yarda da kokarinta rundunan tayi, ya Kuma tabbatar da cewa wannan yabo zai karawa runduna kwarin gwiwa cigaba da gudanar da aiyukanta yadda ya kamata domin ganin an samu ingancaccen tsaro a fadin jahar.




A wata sanarwa da kakakin rundunan ta NSCDC a jahar Adamawa DSC Nyako Amidu Baba yace wannan yabo da gwamna yayi ya nuna cewa rundunan NSCDC ta gudanar da aiyukanta yadda ya kamata a jahar Adamawa.




Yace rundunan zata cigaba da nuna kwarewarta tare da kare martaban bil Adam da Kuma hada Kai da sauran hukumomin tsaro  a wani mataki na Samar da wadaceccen tsaro a fadin jahar. Yabon zai baiwa rundunan damar cigaba da baiwa mazauna jahar ingancaccen tsaro.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.