Gwamnatin jahar Adamawa ta lashi takwabin kare rayuka dama dukiyoyin Al umma................Ahmed Lawan.

 




A wani mataki na inganta tsaro da Samar da zaman lafiya harma da cigaban jahar Adamawa an kirayi daukacin mazauna jahar da sukasance masu baiwa gwamnatin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ya samu damar gudanar da aiyukan cigaban jahar baki Daya.


Mashawarci na musamman akan harkokin tsaro ga gwamna Fintiri na jahar Adamawa Ahmed Lawan ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.



Ahmed Lawan yace Al ummar jahar Adamawa su Sani bamu da wata jahar da ta wuce Adamawa Kuma ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya saboda haka mu nisanta kammu daga dukkanin abinda zai kawo wa jaharmu ko kasarmu koma baya.



Ahmed ya Kuma baiyana cewa Yana da muhimmanci abaiwa gwamnatin hadin Kai kasancewa gwamnati karkashin jagoranci gwamna Fintiri ta dukufa wajen inganta tsaro ba dare ba rana domin ganin ta tabbatar da kare rayuka dama dukiyoyin Al umma baki Daya.


A cewarsa dai jahar Adamawa jaha ce da take na gaba gaba wajen cigaba a fadin Najeriya Kuma jaha ce da Yan kasuwa daga ciki da wajen jahar ke shigowa domin gudanar da harkokin kasuwancinsu harm da zuba jari, saboda kar mu bari wasu suyi amfani da mu wajen lalata jahar mu ko kasarmu.



Ya Kuma godewa Al ummar ta Adamawa musamman ma matasa ganin jahar bata cikin jihohi da aka samu tarzoma saboda haka su cigaba dayin wannan na mijin kokari wajen kare martabar jahar a indon duniya.



Harwayau Ahmed Lawan ya godewa hukumomin tsaro bisa jajircewa da sukayi na ganin ba a samu tashin tashinaba a lokacin zanga zangan kasa da akeyi inda yace wannan abun a yabane.


Ya Kara jaddada cewa gwamnatin jahar Adamawa tana nan da aiki na dare ba rana domin tabbatar da tsaro a fadin jahar da Kuma wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al ummar jahar baki Daya.



Ya shawarci matasa da sukasance masu Neman sana ar dogaro da Kai domin Suma su bada tasu gudumawa wajen cigaban jaha dama kasa baki Daya. Tare da baiwa mazauna jahar shawaran cigaba dayin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro da ciwa gwamnatocin jihohi Dana tarayya tuwo a kwarya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE