Gwamnatin jahar Jigawa ta aiyana ranan talata a matsayin hutu domin bada damar gudanar da bikin cika shekaru 33 da kirkiro jahar.

 






Gwamnatin jahar Jigawa ta aiyana ranan talata 27-8-2024 da ya zama ranan hutu ga ma aikata jahar domin gudanar da bikin cika jahar shekaru 33 da uku da kikiro jahar ta Jigawa.




Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa daga Jami in yada labarain ofishin shugaban ma aikatan jahar  Isma Ibrahim Dutse ya fitar a jahar.




A sanarwar an jiyo shugaban ma aikatan jahar Alhaji Muhammed K Dagaceri na Kiran Al ummar jahar suyi amfani da wannan lokacin wajen yiwa jahar ta Jigawa dama kasa adu o I domin Samar da zaman lafiya dama cigaba.



Sanarwan ta Kuma baiyana cewa dafatan dukkanin ma aikatan jahar zasu Yi amfani da ranan wajen godewa Allah madaukakin sarki taro da adu ar Allah ya kawo zaman lafiya hadin Kai dama cigaba a jahar Jigawa.



Ya Kuma kirayi jama a da su yiwa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a wasu sassan jahar Adu a,  lamarin da yayi sanadiyar rasa rayuka dukiyoyyi masu yawa.



A shekara ta 1991 ne dai aka kirkiro jahar Jigawa karkashin mulkin soja Gen. Ibrahim Badamasi Babangida.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.