Hukumar raya yankin Arewa Masau gabas NEDC zata fara aikin gyaran gadar Waga kamar yadda shugaban kasa ya bada umurnin.




Shugaban kasa  Bola Ahmed  Tinubu ya amince da a gaggauta ginin gadan yankin Wagga na Karamar hukumar Madagali wanda ruwa ya cinye. 




Babban manajan hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas NEDC ,  Mohammed Alkali Goni  ne ya fadi haka yayin hirar shi da manema labaru jim kaɗan bayan duba gadan a Madagali .




Mohammed Alkali Goni yace bayan da shugaban kasa Bola   Ahmed  Tinibu ya samu labarin  wannan ibtila'a, ya amince wa hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas da ta gaggauta fara aikin ginin gadan domin kiyaye karin munin yanayin a yankin.



 

Alkali Goni yayi bayanin cewa lamarin akwai tada hankali matuka ganin ya shafi yadda al'umma ke fita neman halaliyar su  shi yasa shugaban kasa ya gaggauta amincewa da aikin gadar domin kiyaye aukuwar haka nan gaba.



 A cewar babban manajan, tawagar hukumar da masu aikin kwangilar sun iso ne domin gane wa ido , sannan su bullo da dabarbarun da za su taimakawa al'umma nan take, kan a fara aikin ginin gaɗar.





Har wa yau tawagar hukumar da dubi wata gadan dake karamar hukumar Michika wanda itama ta fara yanke wa,  inda babban manajan ya kara bada tabbacin cewa za ayi aikin ta , da duk wasu kwalbatoci dake kan wannan hanyar kamar yadda shugaban kasa ya amince.




Mazauna waɗannan yankuna dama masu ababen hawa da suka tattauna da manema labaru sun baiyana irin wahalhalu da suke fama da sakamakon yankewan wadannan gadojin dama munin hanya.




Sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da na jaha da su taimaka gurin samar da mafitan wannan lamari ganin wannan hanya ne suke bi a kullayaumin domin neman abincin su.



Idan ba a manta ba dai a wata data gabata ne gwamnan jahar Adamawa 

 Ahmadu Umaru Fintiri ya ziyarci yankin na Wagga inda ya dau alkawarin zai tuntube hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas domin daukan matakin gaggawa kan aikin gadar wanda babban hanyar gwamnatin tarayya, mahada na jahohin Adamawa da Borno.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE