Jami ar Modibbo ta samu sabon mataimakin shugaban Jami ar.

 





Biyo bayan zamanta karo na 17 majalisar zantarwar Jami ar Modibbo Adama dake Yola tayi la akari da amincewa da zaban Farfesa Ibrahim Umar a matsayin mataimakin shugaban Jami ar Modibbo Adama Wanda Kuma shine na tara cikin jerin sunayen mataikan shugabannin Jami ar.



Shugaban majalisar zantarwar Kuma pro-chancellor na Jami ar Modibbo Adama dake Yola H. E. Mahmud Aliyu Shinkafi ne ya sanar da haka a kashen taron majalisar 



Farfesa Ibrahim Umar. Farfesa ne a tsangayar kare tsirrai Kuma ya fito ne daga karamar hukumar Gombi dake jahar Adamawa. Kuma ya shugabancin kwalenin fasaha ta jahar Adamawa na tsawon shekaru biyar.



Shugaban sashin yada labarai Jami ar Modibbo Adama Aminu Julde Gurumpawo ne ya baiyana haka a wata sanarwa da aikewa manema labarai a Yola.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE