Kungiyar Fityanu shiyar karamar hukumar yola ta arewa ta kammala horon da tayiwa Yan agajinta.

 




Kungiyar Fityanu shiyar karamar hukumar yola ta arewa ta gudanar da bikin kammala horo da tayiwa Yan agajinta na watanni shida domin karfafa aiyukansu wajen taimakawa Al umma.


A jawabinsa a wajen taron Modibbo Safiyanu Iya Runde wakilain malamai jahar Adamawa Wanda Malam Hayatu iya ya wakilta ya baiyana Jin dadinsa tare da cewa aikin agaji abune da yake da mutukan muhimmanci don haka Yan agajin sukasance masu taimakawa jamma a domin kaucewa shiga matsala.



Modibbo Safiyanu ya Kuma kirayi Al umma musulmai da sukasance masu Neman ilimin addini da na zamani a Koda yaushe domin acewarsa ilimi shine ginshikin duk abinda zai kawo cigaba dama zaman lafiya  da dai sauransu.



Ya Kuma shawarci wadanda aka horar din da suyi amfani da abinda aka koya musu domin ganin an samu cigaban aiyukansu da ma jinkai a tsakanin Al umma baki Daya.


Shima da yake nashi jawabi darektan Yan Agajin Fityanu a jahar Adamawa Mallam Sa idu Modibbo Buba ya baiyana cewa an shirya horon ne domin akarawa Yan agajin kwarin gwiwa tare da dabaru daban daban domin ganin an samu nasaran taimakawa jamm a yadda ya kamata.



Ya kirayi Yan agajin da sukasance masu hada kansu da hakuri da juna domin ganin sun cimma nasaran gudanar da aiyukansu ba tare da matsalaba.







Tunda farko a jawabinsa shugaban kungiyar ta Fityanu a karamar hukumar yola ta arewa Alhaji Sa idu Ardo ya godewa Allah madaukakin sarki da yasa aka kammala horon wa Yan agajin lafiya tare da godewa daukacin wadanda suka halarci bikin, tare da shawartan wadanda suka samu horon da suyi aiki da horon da suka samu tare da fadakar da wasu domin ganin an samu cigaba.




Shugaban karamar hukumar yola ta Arewa Barista Ibrahim Jibrin Wanda kansulan Jambutu ya wakilta Kamal Salihu Don ya yabawa kungiyar bisa wannan na mijin kokari da kungiyar tayi Wanda haka zaitaimaka wajen fadada taimakon Al umma.



Ya Kara da cewa makarantu kiwon lafiya da aka rufe shugaban karamar hukumar zai gana da gwamna domin ganin an samu masalaha an Bude makarantu domin zasu taimaka wajen cigaban kiwon lafiya.


Shi kuwa shugaban majalisar harkokin Addinin musulunci a karamar hukumar yola ta arewa  Abdullahi Butu yace aikin agaji abune da yake da muhimmanci a tsakanin Al umma don haka kada suyi da wasa wajen taimakawa Al umma da Kuma Neman ilimi, Wanda a cewarsa za a samu cigaba yadda ya kamata.


Wakilain Hakimin Nasarawa Abba kira yayi da a cigaba da hada Kai domin ganin an samu zaman lafiya da cigaban Mai daurewa a tsakanin Al umma.



A yayin bikin dai an karma wasu da suka bada gudumawa sosai wajen aiyukan zaman lafiya cigaba da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.