Kungiyoyin NACOMYO Dana YOWICAN sun kaddamar da dashen itatuwa a jahar Adamawa.
A wani mataki na wanzar da zaman lafiya a da hadin Kai a tsakanin Al umma kungiyoyin matasa musulmai wato NACOMYO Dana matasa mabiya addinin kirista YOWICAN sun gudanar da gangamin dashen itatuwa Wanda aka kaddamar a makarantar old G R A dake unguwar NEPA a jahar Adamawa.
Kungiyoyin biyu dai suke sun dauki matakin haka ne domin Samar da zaman lafiya dama hadin Kai a tsakanin Al umma a wani matakin na cigaban jahar Adamawa dama kasa baki Daya.
Da yake jawabi Ko odinata kungiyar NACOMYO a jahar Adamawa Mallam Abdullahi ibn Hamman yace dashen itatuwa abune dake da mutakar muhimmanci don haka akwai bukatar a maida hankali wajen dashen itatuwa domin Samar da zaman lafiya dama hadin Kai a tsakanin Al umma.
Abdullahi Hamman ya jadda aniyar kungiyoyin na gudanar da aiyukan da zai Samar da hadin Kai da zaman lafiya mai daurewa a tsakanin Al umma.
Ya Kuma baiyana cewa zasu fadada wannan dashen itatuwa har zuwa ga daukacin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar Adamawa Wanda acewarsa hakan zai Samar da yanayi Mai kyau ga Al umma.
Shima a jawabinsa Ko odinatan YOWICAN a jahar Adamawa Gabriel yace sun kasance a karantar Old GRA ne domin dashen itatuwa domin inganta muhalli tare da Samar da ingancaccen lafiya a tsakanin Al umma.
Gabriel ya jaddada aniyar kungiyoyin nayin dukkanin abunda suka dace domin wanzar da zaman lafiya mai daurewa a tsakanin Al umma, saboda haka nema yake kira ga Al umma da Suma sukasance suna dashen itatuwa a Koda yaushe.
Itama anata bangaren kwanturola a ma aikatar muhalli ta tarayya Safiya Muhammed Isa Wanda James Adamu ya wakilta ta baiyana gamsuwarsa da Jin dadinta harma da farin cikinta dangane da wannan gangamin dashen itatuwa Wanda acewarta hakan zai taimaka wajen inganta muhalli harma da lafiya ga Al umma.
Ta Kuma shawarci kungiyoyin da sucigaba da wannan aiyukan tasu domin ganin an samu yawan itatuwa a tsakanin Al umma.
Shima mataimakin hedmasta makarantar Tahir Abdullahi Abubakar ya godiya yayiwa kungiyoyin bisa wannan dashen itatuwa da sukayi a makarantar tare da Kiran sauran kungiyoyin da suma suyi koyi da wadannan kungiyoyin domin samun cigaba dama inganta muhalli.
Shikuwa Maisaje Ibrahim Jabir godiya yayiwa shuwagabanin dama membobin kungiyoyin dama duk wadanda suka taimaka wajen wannan gangamin dashen itatuwa tare da fatan dashen zai taimaka wajen Samar da ingancaccen muhalli.
Sama da itatuwa dubu biyu ne dai ake saran kungiyoyi zasu dasa a fadin jahar Adamawa.
Comments
Post a Comment