Kungiyoyin NACOMYO Dana YOWICAN sun shirya taron kan zaman lafiya a jahar Adamawa.
An shawarci Al umma Musulmai da mabiya addinin kirista da sukasance masu hada kansu domin wanzar da zaman lafiya dama daurewan cigaba a jahar Adamawa dama kasa baki Daya.
Mt Morris Vonovalki ne ya bada wannan shawara a lokacin da yake jawabi a wurin taron wanzar da zaman da zaman lafiya Wanda kungiyar matasa Musulmai NACOMYO da na matasa kirista YOWICAN suka shirya a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Morris yace yanzu lokaci yayi da ya kamata a maida hankali wajen Samar da hadin Kai da Kuma kaucewa banbance banbancen addini Dama kabilanci a hadu a Gina kasa domin samu dauwamammen zaman lafiya.
Ya Kuma yabawa kungiyoyin NACOMYO da YOWICAN bisa shirya wannan taro tare da fatan taron zai zama silar Samar da hadin Kai a tsakanin mabiya addinain biyu.
Anasu jawabai shugaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Mallam Gambo Jika da shugaban kungiyar CAN a jahar Adamawa Rev Joel Manzo dukkaninsu sun nuna farin cikinsu da Jin dadinsa dangane da shirya wannan taro tare da Kiran kungiyoyin da su cigaba da yin irin wannan na mijin kokari da sukayi domin ganin an samu cigaban dama zaman lafiya a Mai daurewa.
Da suke nasu jawabai shuwagabanin kungiyoyin wato Mallam Abdullahi ibn Hamman shugabab kungiyar NACOMYO a jahar Adamawa da Mr Gabriel shugaban kungiyar YOWICAN a jahar Adamawa. sun baiyana cewa sun shirya wannan taron ne da zumar wanzar da zaman lafiya mai daurewa a tsakanin mabiya addinain biyu.
Kuma sun yabawa wadanda duk suka halarci taron tare da Kiran mahalarta taron da suyi amfani da abinda suka ji a wurin taron domin Samar da cigaban zaman lafiya.
Da yake nashi jawabi John Gamsa ya godewa kungiyoyin dangane da shirya wannan taro tare da ahawartansu da su cigaba da irin wannan aiyuka da zaitaimaka wajen hadin kan Al umma da Kuma cigaba.
Gwamna Ahmadu Fintiri na jahar Adamawa Wanda mataimaki na musamman akan harkokin addinin Malam Ali Mamman ya wakilta Kiran matasa yayi da sukasance masu hada kansu da Kuma Neman sana o I da zasu dogara da kansu.
A cewarsa gwamnatinsa tana iya kokarinta domin ganin matasa sun tsaya da kafafunsu ta wajen Samar musu da sana o I daban daban a fadin jahar.
Shima anaahi bangaren Wafari Theman shawartan matasan yayi da Suma sukasance suna bada tasu gudumawa wajen aiyukan hadin Kai da wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al umma.
Comments
Post a Comment