Majalisar matasa Musulmai a Najeriya NACOMYO ta nisanta kanta daga zanga zanga da akeyi a fadin Najeriya.






 Majalisar matasa musulmai a Najeriya shiyar jahar Adamawa  NACOMYO ta nisanta kansa daga zanga zangan lumana da wasu matasa da ma kungiyoyi suka kudiri aniyar yi a fadin Najeriya.



Ko odinetan majalisar a jahar Adamawa Alhaji Abdullahi ibn Hamman ne ya baiyana haka a taron manema labarai da ya gudanar a Yola.



Alhaji Abdullahi Hamman yace a matsayin majalisar matasa musulmai basu amince da zanga zanga ba saboda zanga zanga a addinin musulunci jaramunne, saboda  haka basuga dalilin da yasa zasu Sa kansu cikin yin zanga zangan ba.


Ibn Hamman yace yin zanga zanga ya saba karantarwan addinin musulunci domin a cikin Al Qur ani Mai girma da hadisi duk sun la anci zanga zanga misalin a cikin Al Qur ani sura ta 5 aya ta 32 da sura ta 2 Aya ta 208 duk suyi hani kan tada husuma saboda haka suna masu Allah wadai da shirya wannan zanga zanga.



Ko odinaton yace musulunci Yana karantar da zaman lafiya da Kuma hadin Kai saboda haka majalisar matasa. ta musulmai  wato NACOMYO bata goyon bayan zanga zanga da aka shirya Yi daga ranan 1-10-8-2024.



Majalisar tace tana da yakinin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Yan bukatan Karin lokaci daga Yan Najeriya Kuma majalisar ta baiyana cewa shugaban kasan yayi abin Azo a gani a shugabancinsa domin yayi kokarin wajen baiwa kananan hukumomin yancinsu, da Karin Albashi mafi karanci, bada Rance ga dalube domin yin karatu, cire haraji daga kan kayakin abinci dama mahimmain aiyuka.



Haka kazalika majalisar ta kirayi gwamnatin da ta taimaka wajen rage radadin wahala rayuwa da Yan Najeriyan ke fuskanta. Majalisar ta Kuma yabawa shuwa gabanin addinai da malamai bisa shiga tsakani tare da yin adu o I saboda haka nema suka kirayi shuwagabanin da su fadada zuwa Yan siyasa da su kasance masu taimakawa matasa dama marassa galihu. Majalisar ta Kuma mika yabonta ga sarakunan gargajiya bisa rawa da suke takawa wajen Samar da zaman lafiya tare da Kiran su da sukasance masu bada shawaran ganin an taimakawa marassa galihu.




Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE