Makarantar Sabilur Rashad ta cika shekaru 20 da kafuwa.
Makarantar Sabilur Rashad dake cikin karamar hukumar yola ta kudu tayi bikin cika shekaru 20 da kafuwa Wanda Kuma bikin ya samu halartan Jama a da dama wadanda suka fito daga ciki da wajen jahar Adamawa.
Farfesa Abdullahi Liman Tukur tsahon mataimakin shugaban. Jami ar Modibbo Adama dake nan Yola Wanda Kuma shine Bako Mai jawabi a wurin bikin ya ja hankalin Al umma da sukasance masu maida hankali wajen baiwa yara ilimi kasancewa sune shuwagabanin gobe
Liman Tukur Wanda Dr Abubakar Bello Jada ya wakilta yace Ilimi Yana da mutukan muhimmanci saboda haka kar ayi da wasa wajen baiwa ilimi muhimmanci Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen rage yawan yaran da basu zuwa makarantar.
Ya Kuma yabawa makarantar ta Sabilur Rashad bisa na mijin kokari da sukayi na ganin cewa yara sun Sami ingancaccen ilimi saboda haka nema yake kira ga sauran makarantu da suyi koyi da makarantar Sabilur Rashad domin ganin an samu damar bunkasa ilimi a tsakanin yara.
Ya yabawa malamai bisa hakuri da juriua da suke dashi wajen karantar da yara tare da Kiran iyaye da sukasance suna baiwa malamai hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran baiwa yaransu ingancaccen ilimi.
Shugaban kungiyar Izala na kasa Sheirk Abdullahi Bala Lau Wanda Mallam Ali Mamman ya wakilta ya yabawa makarantar ta Sabilur Rashad bisa cika shekaru 20 da kafuwa Wanda yace wannan ba karamin nasarabace ganin irin jajircewa da makarantar tayi tana karantar da yara har na tsawon shekaru 20 saboda haka makarantar tayi abun Azo a yaba.
Mallam Ali Mamman ya Kuma shawarci iyaye da sukasance masu hada kansu da malamain makarantar domin ganin sun cimma burinsu na karantar da dalube yadda ya kamata.
Ya Kuma godewa Hajiya Maryam Babalau Hassan bisa kokarinta na assasa wannan makarantar tare da fatan sauran mata zasuyi koyi da ita.
Shugaban karantar Sabilur Rashad Malam Musa Hamman yace makarantar Sabilur Rashad ta cimma nasarori da dama da suka hada da yaye ingantattun dalube Kuma suna da dakin gwaje gwaje tare Kuma da samun izinin samun cibiyoyin rubuta jarabawan kammala sakandare wato WAEC da NECO da dai sauransu.
Ya Kuma kirayi Al umma musammanma iyaye da sukasance masu baiwa makarantar hadin Kai da goyon baya domin makarantar da samu nasara baiwa dalube ilimi Mai inganci.
Mallam Gidado Babalau Hassan shine darektan Makarantar ta Sabilur Rashad ya zanyano tarihin makaratar inda yace an Samar da makarantar ta Sabilur Rashad ne tun a shekara ta 2003 Wanda Kuma an farane da dalube kalilan Wanda Kuma kawo Yan makarantar tana da dalube da dama tare da yaye da dama daga cikinsu.
Kawo yanzu makarantar tana da cibiyoyin rubuta jarabawan kammala sakandare tare da zauren rubuta jarabawan Kuma tana samun nasarori a bangaren daban daban da suka hada dana kimiya da fasaha da dai sauransu.
Mallam Gidado Babalau yace makaratan harma tana bada gurbin karatu ga dalube marassa galihu kauta saboda haka akwai bukatar a baiwa makarantar hadin da goyon baya a Koda yaushe domin ganin ya samu nasara yadda ya kamata.
Dake yake nashi jawabi Mai martaba Lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa Wanda Hakimin Yola Alhaji Zubairu Adamu Mustafa ya wakilta ya jinjinawa Hajiya Maryam Babalau bisa kokarinta na kada wannan. Makarantar Wanda acewarsa wannan ba karamin cigaba bane a cikin Al umma.
Yace ya kamata a samu mata da dama da Suma zasuyi kokayi da Hajiya Maryam wajen Bude makarantu Wanda hakan zai taimaka wajen cigaban ilimi a jahar da ma kasa baki Daya.
Itama anata bangaren Hajiya Rukaiyya Atiku Abubakar Wanda Hajiya Fati Girei ta wakilta ta ta nuna Jin dadinta tare da yabawa Hajiya Maryam Babalau dangane da kafa wannan makarantar Wanda a cewarta wannan ba karamin nasara bane a tsakanin Al umma, saboda haka a kwai bukatar iyaye su bada tasu gudumawa wajen cigaban makarantar a Koda yaushe.
Bayan karatuttuka da wake wake da daluben Makarantar suka gudanar an karrama malamain makarantar da lambar yabo tare da baiwa dalube kaututtuka ga wadanda sukayi samun nasaran samun lambar Daya zuwa uku.
Comments
Post a Comment