PCRC dake Jambutu sun junjinawa rundunan yan sandan jahar Adamawa.

 





Al umma dake taimakawa rundunan Yan sanda wato PCRC shiyar anguwar Jambutu ta yabawa rundunan Yan sandan jahar Adamawa  bisa kokarinta na inganta tsaro a lokacin zanga zangan kasa da ya gudana a fadin Najeriyar.



Shugaban PCRC dake Jambutu Alhaji Adamu Jingi Wanda akafi sani da Mai hange ne ya yi wannan yabo a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.



Alhaji Adamu Jingi yace rundunan yan sandan ta taka rawan ganin wajen inganta tsaro a lokacin zanga zangan a jahar Adamawa saboda haka rundunan ta cancanci yabo saboda irin wannan na mijin kokari da rundunan Yan sandan tayi.


Alhaji Adamu ya Kuma baiyana cewa  yabon Gwani ya zama dole domin rundunan yan sandan karkashin jagoranci kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris tayi kokari wajen kare rayuka dama dukiyoyin Al umma a fadin jahar Adamawa.



Adamu Jingi ya Kara da cewa PCRC dake shiyar Anguwar Jambutu a shirye take ta baiwa rundunan Yan sandan hadin Kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran kare rayuka da ma dukiyoyin Al umma 


Ya Kuma shawarci daukacin Al umma dake fadin jahar ta Adamawa da sukasance masu taimakawa rundunan Yan sandan da wasu baiyanai da zai basu damar kakkabe matsalar tsaro a fadin jahar Adamawa baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE