PCRC ta yabawa rundunan Yan sandan jahar Adamawa.

 




Al umma dake taimakawa Yan sanda wato PCRC shiyar jahar Adamawa sun yabawa rundunan Yan sandan jahar Adamawa bisa nuna kwarewarsu a lokacinda aka gudanar da zanga zangan kasa.




Kakakin rundunan yan sanda a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.





Shugaban Al umma dake taimakawa rundunan Yan sanda Hon. Musa Bubakari Kamale da yake mikawa kwamishin Yan sandan na jahar Adamawa Dankwambo Morris takardan yabon a shelkwatan rundunan yan sandan dake Yola,

ya baiyana cewa rundunan tayi abin Azo a yaba saboda haka ya zama wajibi a yabawa rundunan bisa na mijin kokari da sukayi na inganta tsaro da Kuma nuna kwarewarsu wajen kula da yadda aka gudanar da zanga zanga.




PCRC sun Kuma jinjinawa rundunan bisa kokarinta na wanzar tare da tabbatar da zaman lafiya da Kuma ganin an kammala zanga zangan ba tare da matsalaba.




Da yake karban takardan yabon Kwamishinan Yan sanda Dankwambo Morris ya yaba da irin wannan karramawa da PCRC sukayiwa rundunan yan sandan.




Ya Kuma tabbatarwa Al ummar jahar Adamawa cewa rundunan a shirye take ta cigaba da kare rayuka dama dukiyoyin Al umma dake fadin jaha domin Samar da zaman lafiya a fadin jaha.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE