Rikici a tsakanin manoma da makiyaya yayi sanadiyar mutuwar mutane uku a jahar Adamawa.
Kawo yanzu dai kura ta lafa a yankin Kodomun biyo bayan tashin hankali da aka samu a tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Demsa dake jahar Adamawa, acewar rundunan yan sandan jahar Adamawa.
Rundunan Yan sandan ta baki kakakinta SP Suleiman Yahaya Nguroje yace yanzu kowa na gudanar da harkokinsu yadda ya kamata domin an tura Jami an tsaro a inda lamarin ya faru.
SP Suleiman Yahaya Nguroje ya baiyana cewa tunin kwamishinan Yan sanda jahar ya Adamawa Dankwambo Morris ya bada umurnin gudanar da bincike dangane da lamarin.
A cewarsa tunin aka kama mutane uku da ake zargi da hanu a rikicin Wanda a yanzu haka ana gudanar da bincike akansu. Tare da Kiran dukkanin masu ruwa da tsaki su taimaka wajen magance matsalar baki Daya.
Rikincin dai yayi sanadiyar mutuwar mutane uku tare da asaran dukiyoyi masu yawa.
SP Suleiman Yahaya ta Kuma shawarci Al umma da su daina daukan doka a hanu su rinka Kai rahoton dukkanin abinda basu yarda daahiba zuwa ga ofishin hukumomin tsaro.
Comments
Post a Comment