Rundunan tsaron Civil Defence dake jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin kare rayuka da dukiyoyin Al umma.
Rundunan tsaro dake bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence a Najeriya shiyar jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin bada kariya da Kuma ganin an gudanar da zanga zangan lumana cikin tsanaki na tare da wata matsalaba a fadin jahar Adamawa.
Kakakin rundunan a jahar Adamawa DSC Nyako Amidu Baba ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake Yola.
DSC Amidu yace tuninma suka tura Jami ansu a muhimmain wurarai domin ganin ba ayiwa Al umma barnan kayakinsu saboda sun dauki dukkanin matakai da suka gabata domin ganin an kammala zanga zangan lafiya.
Ya Kuma tabbatar da cewa rundunarsu Daman tun daga lokacinta aka fara maganan shirya wannan zanga zanga bata barci da idonta biyu inda ta kudiri aniyar ganin ba a samu tsekoba.
DSC Nyako ya tabbatarwa Al ummar jahar Adamawa cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin daukacin Al ummar dake fadin jahar domin ganin an samu zaman lafiya mai daurewa a fadin jahar baki Daya.
Harwayau ya shawarci jama a da sukasance masu taimakawa rundunan tasu da wasu baiyanai da zai basu damar dakile aikata laifuka a tsakanin Al umma.
Comments
Post a Comment