Rundunan Yan sanda jahar Adamawa ta karawa Jami anta 120 Karin girma na mataimakin safritandan.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya likawa Jami an Yan sanda Dari da ashirin girma a matsayin mataimaka safritandan Yan sanda.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Karin girman ya biyo bayan amincewa da hukumar aiyukan Yan sanda wato PSC tayi dukkanin Jami an Yan sanda 120 da suka samu Karin girma da sifeta zuwa matakin safritandan a jahar Adamawa wato ASP an basu ne bisa kwarewa da cancantansu .
Kwamishinan ya taya su murnan samun wannan mukami tare da ahawartansu da suyi amfani da mukamin da suka samu ta hanyar da suka dace da Kuma bin dokokin aiki tare dayin abinda zasu samu yabo daga Al umma, tare da gudanar da adalci a yayin aiyukansu da dai sauransu.
Bayan ga tawagan kwamishinan Yan sanda Yan uwa da abokan Arziki sun halar bikin likawa Jami an Yan sandan mikamin Wanda akayi Police officers mess dake nan Yola.
Comments
Post a Comment