Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta umurci Jami anta da su tabbatar abi dokan hana Bola Bola a fadin jahar.
Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta murcin manyan Jami anta dake ofisoshinta a fadin jahar Adamawa da su tabbatar abi dokan nan da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sanyawa hanu na haramta aiyukan bala bala a fadin jahar.
Kamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ne ya baiyana haka a wata sanarwa daga kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya rabawa manema labarai a Yola.
Umurnin ya shafi dukkanin kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar har zuwa wani lakoci da ba a baiyanaba.
Kwamishinan Yan sandan yace duk Wanda aka samu da aiyukan Bola Bola daga ran 15-8-2024 to ya aikata laifi za a kamashi Kuma a gurfanar dashi a gaban kotu.
Kawo yanzu dai rundunan ta baza Jami anta domin Saka kafar wando Daya da duk Wanda yayiwa dokan biris, saboda haka dokan zatayi aiki akan Wanda ya yiwa doka Karan tsaye.
Saboda haka rundunan ta gargadi dukkanin masu aikata Bola Bola da su nisanta kansu su baiwa hukumomin tsaro da aka tura domin ganin anbi dokan hadin Kai da goyon baya. Domin rundunan bazata lamuntaba.
Comments
Post a Comment