Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin tinkara zanga zangan lumana
Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin ganin ba a samu wata hayaniyaba a lokacin gudanan da zanga zangan lumana da wasu kungiyoyin matasa da suka kitsayi da sunan kawo karshen matsanancin rayuwa da ake fuskanta a fadin Najeriya.
Rundunan ta baiyana haka ne ta bakin kakainta SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake Yola.
Kakakin rundunan. yace kawo yanzu dukkanin matakai da ya kamata a dauka sun dauka domin ganin zanga zangan ya tafi cikin lumana ba tare da an jikkata kowaba.
SP Suleiman tuninma suka kafa shingen binciken ababen hawa a dukkanin mashigan fadar gwamnatin jahar domin ganin an Samar da zaman lafiya a tsakanin Al umma.
Nguroje yace Yana daga cikin matakai da suka dauka na tura Jami an su zuwa sako sako domin sanya ido akan dukiyoyin Al umma da Kuma baiwa jama a kariya a duk inda suke a fadin jahar.
SP Suleiman Yana Mai tabbatarwa Al ummar jahar ta Adamawa cewa rundunan bata barci da idonta biyu yanayin dukkanin maiyiwa domin ganin ta kare rayuka dama dukiyoyin Al umma.
Saboda haka nema ya kirayi Al umma da sugudanar da harkokinsu na yau da killum domin rundunan ta baza Jami anta harma da komarta domin Saka kafar wando Daya da duk Wanda zaiyiwa doka Karan tsaye.
Ya Kuma shawarci kungiyoyin matasan da suka shirya zanga zangan da kada su wuce gona da iri domin rundunan bazata lamucewa duk Mai yiwa zaman lafiya narazanaba, don haka ya kamata a kiyaye.
Harwayau ya kirayi Al umma da a Koda da yaushe sukasance masu taimakawa rundunan Yan sandan da wasu bayanain sirri da zai basu damar dakile ko kama masu aikata laifuka a duk inda suke.
Comments
Post a Comment