Sabon kwamandan Rundunan tsaro na Civil Defence a jahar Adamawa ya kama aiki.

 





Rundunan tsaro bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence shiyar jahar Adamawa ta marabci  sabon kwamandan ta Idris D Bande Wanda tuninma ya fara aiki a hukumance Jin kadan da karabar ragamar shugabancin rundunan daga Wanda ya gada Ibrahim Mainasara. An dai bikin marabtar sabon kwamandan ne a shelkwatar rundunan ta NSCDC dake nan Yola.




Kakakin rundunan. ta NSCDC a jahar Adamawa DSC Nyako Amidu Baba ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola. Fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Sabon kwamandan dai an sauya masa wurin aiki ne daga yankin B dake jahar Kaduna Wanda ya maye gurbin Ibrahim Mainasara Wanda yayi aiki na tsawon shekara Daya da watanni uku Kuma shine kwamandan rundunan na 15 a jahar Adamawa.



A lokacinda yake mika ragabab shugabancin rundunan ga sabon kwamandan Ibrahim Mainasara ya kirayi dukkanin Jami an rundunan da su baiwa sabon kwamandan cikekken hadin Kai da goyon baya domin tabbatar da ganin cewa rundunan ta cigaba da gudanar da aiyukan da suka dace ga Al umma. Ya Kuma baiyana cewa Yana da yakinin cewa sabon kwamandan wato Idris D Bande zai jagoranci rundunan yadda ya kamata da Kuma yin abinda zai kawo cigaban rundunan a fadin jahar.




Da yake nashi jawabi bayan ya karbi ragamar shugabancin Runduna Sabon Kwamandan Bande ya baiyana godiyarsa da jindadinsa dangane da yadda aka marabceshi ya Kuma Yi alkawarin dorawa daga inda Wanda ya gada ya tsaya ya Kara da cewa zaiyi dukkanin abinda suka dace domin inganta aiyukan rundunan domin Samar da wadaceccen tsaro a fadin jahar Adamawa.



Rundunan ta NSCDC dake jahar Adamawa dai ta tabbatar da cewa sabon kwamandan Bande zai gudanar da shugabancin Rundunan ta Samar da dabaru dama tsare tsare da zai taimakawa rundunan damar kare rayuka dama dukiyoyin Al umma dake fadin jahar ta Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE