Sarkin Ningi ya rasu Yana da shekaru 87.
Rahotanni daga jahar Bauchi na cewa Allah yayiwa Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammed Danyaya tasuwa.
Basaraken ya rasune a wani asibiti dake Kano bayan kwanaki biyu da ya dawo daga duba lafiyarsa a kasar Saudiya.
Kuma ya rasu Yana da shekaru 87 da haifuwa.
Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa daga sakataren fadar Alhaji Usman Sule magayaki Ningi. Tare da baiyana cewa za ayi jana izarsa da misalin karfe 4:00 na yamma a fadarsa dake Ningi.A Ladin nan 25-82024.
Comments
Post a Comment