Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar Aikin hajji ta kasa. NAHCON.
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da nada Farfesa Abdullahi Sale Usman a matsayin shugaban hukumar Aikin Hajji ta kasa wato NAHCON.
Mashawarci na musamman kan harkan yada labarai ga shugaban kasa Ajuri Ngelale ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitara a litinin din nan.
Nada sabon shugaban na zuwa ne bayan sallama shugaban Hukumar ta NAHCON Malam Jalal Arabi Wanda shugaban kasar ya sallama biyona zarginsa da almudahana da kudin da yaki nera bilyon 90 Wanda gwamnatin tarayya ta baiwa hukumar a matsayin tallafi ga aikin hajjin shekara ta 2024.
An sallami Jalal daga kan mikamin shugabancin hukumar aikin hajji ta kasan ne bayan kwanaki hudu da hukumar dake yaki da cinhanci da rashawa wato EFCC ta kamashi bisa tukumarsa da yin na daidaiba da kudaden hukumar.
Shugaban kasa yace Yana Mai tsammanin sabon shugaban zai gudanar da aiyukansu yadda ya kamata domin inganta hukumar.
Comments
Post a Comment