Yan sanda biyu sun gamu da ajalisu tare da jikkata uku a wani hari da aka Kai akan Jami an Yan sanda a Abuja.
Jami an Yan sanda biyu ne suka rasa rayukansu a yayinda uku suna cikin wani yanayi na jikkata tare da cinnawa motoci Yan sandan wuta, sakamokon hari da ake zargin mabiya darikar shiya ne suka kaiwa Yan sanda a dai dai lokacinda suke gudanar da aiyukansu a shingen binciken ababen hawa dake mahadar wusai a birnin tarayya Abuja.
Kakakin rundunan. Yan sandan Abuja SP Josephine Adeh ta baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a madadin kwamishinan Yan sandan na Abuja.
Kwamishinan Yan sandan Abuja Benneth C Igweh yayi Allah wadai da wannan hari na rashin tausayi da aka kaiwa Yan sanda tare da yin alkawarin hukunta duk Wanda aka samu da laifin akata haka inda yace kawo yanzu komai Yana tafiya dai dai a inda lamarin ya faru.
Comments
Post a Comment