Ambaliya: An shawarci Al umma daina tushe magudanain ruwa.

 




A wani mataki na inganta harkokin noma da Kuma kaucewa ambaliyar ruwa an kirayi gwamnatoci a dukkanin matakai dama masu ruwa da tsaki da Al umma da sukasance masu aiki kafada da kafada domin magance matsalar baki Daya.


Kwamandan Mafarauta na kasa Kuma Sarkin yakin mafarautar jahar Adamawa Alhaji Muhammed Adamu ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai dangane da harkokin noma dama ambaliya.


Alhaji Muhammed Adamu yace yana da muhimmanci gwamnatin tarayya Dana jihohi har da na kananan hukumomi da su Kara himma wajen yiwa Al umma ingantattun mugadanen ruwa Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen kariya daga ambaliyar ruwa, dake janyo asarar masu yawa da suka hada dana rayuka da dukiyoyi da dai sauransu.



Alhaji Muhammed ya Kuma shawarci Al umma da su guji zuba shara a magudanen ruwa Mai makon hakama sukasance masu tsafcace mugudanen ruwa domin toshe mugudanen ruwa shine yake sanadiyar ambaliyar ruwa don haka jama a su guji toshe magudanen ruwa.


Alhaji Muhammed Adamu ya ya baiyana farin cikinsa dangane da yadda aka gudanar da harkokin noman damina tare da yin adu ar Allah madaukakin sarki ya taimaka ya bada damina Mai albarka da Kuma kammalashi lafiya.


Alhaji Adamu ya jajintawa jihohi da suka fuskanci ambaliyar ruwa da suka hada da Adamawa, Borno, Bauchi, Yobe, Neja, Sokoto, Katsina, Kaduna, Taraba, Nasarawa, Gombe, da dai sauransu.



Ya Kuma mika jajensa na musamman ga gwamnatin jahar Borno da daukacin Al ummar jahar bisa iftila I da ya faru na ambaliyar ruwa a cikin garin Maiduguri da fatan Allah ya kare ya Kuma mayar musu da abinda suka rasa. Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, ya baiwa wadanda suka jikkata sauki.




Harwayau Alhaji Muhammed Adamu ya kirayi Al umma musamman na Sabon Birni Gwaranyo wadanda sunyi wasu shekaru 2-3 basu samu damar nomaba saboda matsalar tsaro sai bana to sukasance suna baiwa Mafarauta dama hukumomin tsaro hadin Kai da goyon baya a Koda yaushe domin ganin an magance matsalar tsaro a yankin dama kasa baki Daya.




Yace  baiwa hukumomin tsaro da Mafarauta hadin Kai Yana da muhimmanci saboda haka Al umma kada suyi kasa a gwaiwa wajen bada hadin Kai da goyon baya ta taimakawa da wasu bayanain sirri da zai baiwa ma aikata takawa matsalar birki.



Ya Kuma yabawa gwamnati bisa kokari ta yakeyi na inganta tsaro tare da Kiran ta da ta Kara kaimi wajen baiwa bangaren tsaron muhimmanci domin magance matsalar baki Daya ya Kuma shawarci gwamnatin da tayi dukkanin maiyiwa domin ganin an samu saukin rayuwa a tsakanin Yan Najeriya baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE