Hukumar kare haddura ta tarayya ta kudiri aniyar inganta aiyukan matuka matocin kasuwa a fadin jahar Adamawa.

 




Sabon Kwamandan hukumar kare haddura ta   tarayya a jahar Adamawa C C Yahaya Sabo Adikwu ya baiyana cewa ahirinsa shine Samar da tsari da zaitaimaka wajen inganta harkokin tuki domin kaucewa yawan samu cinkoso ababen hawa a fadin jahar. 



Ya baiyana cewa da farko zai gabatar da sabon tsari kan tukin motocin kasuwa ta Samar musu da kaya bai Daya Wanda hakan zai basu damar gane duk wata kamfanin sifiri.



Ya kara da cewa zasu gabatar da wayar da Kai da horo ha matukan motocin kasuwanci domin kautata aiyukansu dama fasinjojinsu.



A cewarsa dai Yana so ya inganta harkokin tuki a fadin jahar dama inganta aiyukansu yadda ya kamata.tare da mutunta fasinjojinsu dama nuna da a a tsakanin Al umma 



Kwamandan yace a lokacin gangamin imba months da zasu na wayar da Kai a tashoshin motoci zasu hada Kai da hukamar NDLEA domin  gwajin miyagun kwayoyi Kuma duk direban da suka samu Yana ta ammali da miyagun kwayoyi zasu turasu waje da za sauya masa tunaninsa domin rage yawan hadura a kan hanyoyin.



Ya kirayi kungiyoyi dama  bangarorin masu zaman kansu harma da gwamnatoci da su taimakawa hukumar ta FRSC da wasu kayakin aiki da zai bada damar gudanar da aiyukanta domin ganin ta samu nasaran aiyukan da tasa a gaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE