Jami an Yan sanda sun samu Karin girma a jahar Adamawa.

 



Jami an Yan sanda goma Sha biyu sun samu Karin girma a rundunan yan sandan jahar Adamawa daga mukamain safirtanda zuwa Babban safirtanda.


Da yake lika musu mukamain kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya kirayi wadanda suka samu Karin girman da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa doka da Kuma kwarewa da suke dashi domin ganin an samu cigaba tsaro dama zaman lafiya mai daurewa a tsakanin Al umma.


Ya Kuma yabawa Jami an Yan sanda bisa sadakarwa da suke wajen kare rayuka dama dukiyoyin Al umma dake fadin jahar baki Daya.



An dai gudanar da bikin lika mukamain ga Yan sandan ne a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE