Kungiyar CONASAI ta lashi takwabin yaki da ta ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin Al umma dake fadin Najeriya.
Kungiyar dake fafutukan yaki da ta ammaki da miyagun kwayoyi a tsakanin Al umma wato CONASAI tace zata shirya ta rurrukan wayarwa Al umma Kai a wurare daban daban da suka hada da tashoshin motoci, kasuwanni, wuraren taron jama a da dai sauransu a wani mataki na dakile shaye shayen miyagun kwayoyi a cikin Al umma baki Daya.
Kungiyar ta shugaban ta na kasa Dr Jalo Jauro yace kungiyar zatayi aiki kafada da kafada da kungiyoyi daban daban, sarakunan gargajiya, shuwagabanin addinai, masu ruwa da tsaki domin daukan matakin magance matsalar shaye shaye a tsakanin Jama a musammanma matasa.
Dr Jalo Jauro yace kungiyar zata Kuma hada Kai da masu ruwa da tsaki, sarakunan gargajiya, shuwagabanin addinai Wanda hakan zai taimaka wajen dakile matsalar baki Daya.
Don haka nema ya kirayi masu ruwa da tsaki, sarakunan gargajiya, kungiyoyin fararen hula shuwagabannin addinai da sukasance masu baiwa kungiyar ta CONASAI hadin Kai da goyon baya domin ganin ta cimma manufarta na yaki da ta ammali da miyagun kwayoyi domin Samar da zaman lafiya da Kuma cigaba a fadin kasannan baki Daya.
Dr Jalo ya Kuma kirayi iyaye da su maida hankali wajen kula da yaransu a Koda yauce domin a cewarsa iyaye suna da rawa da zasu iya takawa dakatar da ta ammali da miyagun kwayoyi a fadin kasan nan.
Yama shawarci matasa da su nisanta kansu daga Shan duk abinda zai gusar musu da hankali domin samun cigaba da zaman lafiya a tsakanin Al umma.
Harwayau Dr Jalo ya kirayi dukkanin membobin kungiyar ta CONASAI da sukasance masu gudanar da aiyukansu bi hakki da gaskiya da jajircewa da hakuri tare cigaba dayin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki a Koda yaushe domin ganin gunkiyar taci nasaran aiyukanta yadda ya kamata.
Comments
Post a Comment