Kungiyar Yan Jarida NUJ shiyar jahar Adamawa ta Taya gwamna jahar Adamawa dama Al ummar jahar murnan bikin Maulidi.

 





Kungiyar Yan jarida a Najeriya N U J shiyar jahar Adamawa tana Mai taya gwamnan jahar Adamawa  dama daukacin Al umma musulmai dake fadin jahar Adamawa murnan bikin Maulidi wannan shekara ta 2024.




Kungiyar ta baiyana haka ne a wata sanarwa da ake rabawa manema labarai dauke da sanya hanun shugaban kungiyar a jahar Adamawa Ishayaku Donald Dedan da sakatarenta Fedelis Jocthan da suka fitar a Yola.




Kungiyar ta Kuma taya membobinta murnan bikin Maulidi ranan haifuwar fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu S A W.



A yayin bikin an kirayi dukkanin Al umma da suyi koyi da jalayen manzon Allah domin ganin an samu zaman lafiya da fahintar juna harma da cigaba.




Kungiyar ta Kuma kirayi Al umma musulmai da suyi amfani da wannan lokaci wajen yin adu o I Samar da hadin Kai da Kuma samun moriyar domokiradiya kamar yadda muke ganin cigaban domokiradiya a jahar Adamawa karkashin shugabancin  gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.




Sanarwan ta Kuma shawarci kafafen yada labarai sukasance masu maida hankali wajen abinda zai taimaki jama a a rahotaninsu domin kautata walwaln ma aikata da suka hada da na gwamnati da masu zaman kansu.



Kungiyar ta Kuma Yi adu ar Allah yasa a gudanar da bikin Maulidi lafiya da lumana a fadin jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE