Matsalar Wutan lantarki: Daluben kwalejin fasaha na jahar Adamawa sun gudanar da zanga zangan lumana.
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
Da sanyar safiyar Litinin din nan ne dai daluben kwalejin fasaha ta jahar Adamawa suka gudanar da zanga zangan lumana a wani abunda suka kira da rashin wutan lantarki a makarantar dama matsalar rashin ruwa Wanda acewarsa sun dauki dauki tsawon makwanni biyu batare da wutan lantarki ba.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a madadin daluben Baba Lastiri ya baiyana damuwarsa dangane da rashin wutan dama ruwa tare da Kiran gwamnatin jahar Adamawa dama hukumar gudanarwan makarantar da su dauki matakan gaggawa domin magance matsalar baki Daya.
A cewarsa lamarin da yasa sai daluben sun fita wajen makarantar kafin debo ruwa saboda su sun gaji da haka saboda haka ne suke bukatar hukumomi suyi dukkanin Mai yiwa domin kawo karshen matsalar baki Daya.
Shima a jawabinsa shugaban kwalejin Farfesa Muhammed Tangos ya sanar da cewa kawo yanzu an shawo kan matsalar domin a cewarsa hukumar gudanarwan kwalejin suna iya kokarinsu domin ganin komai ya daidaita a kwalejin.
Shugaban kwalejin yace Yana Mai tabbatarwa Al umma cewa matsalar wutan Kam an shawo kan matsalar Kuma da yardan Allah komai zai koma daidai na tare da wata matsalaba.
Comments
Post a Comment