Mazauna gidan yari 42 sun samu afuwa a yayinda aka nada belin 25 a jahar Adamawa.

 




Kwamitin kan gidan yari a jahar Adamawa Wanda shugabar Alkalain jahar Adamawa maisharya Hafsat Abdulrahman ke jagoranta ya sallami mazauna gidan yari 42  tare da bada belin mutane 25 da Kuma yankewa mutane 37 hukunci a gidan yarin Yolde Pate dake Yola.




Cikin mazauna gidan yari 182 da suke jiran shariya wadanda aka ganatarwa kwamitin an sallami mutane 32 tare da yankewa mutane 37 hukunci. An Kuma sake sallaman mutane 10 daga cikin wadanda aka yankewa hukunci.




Wasu daga cikin wadanda aka sallama an sallamesune biyo bayan yadda laifukansu basu taka Kara sun karyaba.



Kwamitin ya dauki matakin haka saboda rage cinkoso a gidajen yari dake fadin jahar.



Mazauna gidan yari 800 ne dai ake bukatar zamansu amman yanzu haka mazauna gidan yarin sunkai 886.



A cikinsu akwai 665 suna jiran shariya a yayinda 185 an yanke musu hukunci da Kuma 10 na jiran hukucin Rai da Rai sai Kuma 16 na fuskantar hukuncin kisa.




Kwamitin yace anyi rijistan kasa kasai da yawa wandan da kwamitin zaiyi la akari da su amman Banda laifin kisa, laifin garkuwa da mutane. Aiyukan zai ta allakane kan wadanda suke jiran shariya da Kuma wadanda aka yanke musu hukunci.



Shugabar Alkalain ta taya wadanda suka samu yancinsu murna tare da gargadinsu da su nisanta kan da aikata laifuka.



Ta Kuma kirasu da suyi amfani da wannan yanci da suka samu na damane a garesu da zasu samarwa kansu abinda zasu inganta rayuwarsu.



Da yake magana a madadin wadanda aka sallama Dominic David yayi alkawarin cewa zasuyi dukkanin maiyiwa domin inganta rayuwarsu.



Ya Kuma yabawa shugabar Alkalain da tawaganta David yace dafatan hakan zai taimaka musu wajen daga martabansu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE