Mutane 26 sun Samu yanci daga gidan yarin cikin garin Yola dake jahar Adamawa.
A cigaba da ziyar gidan yari da kwamitin kan harkokin shariya keyi, kwamitin karkashin jagoranci shugabar Alkalain jahar Adamawa Maisjariya Hafsat Abdulrahman ya sallami mutane shida daga gidan yarin cikin garin karamar hukumar yola ta kudu tare bada belin mutane 13 da Kuma yankewa akalla mutane 6 hukuncin zama a gidan yari.
Daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin an saki goma a yayinda ake duba laifukan mutane tara daga cikin mutane 128, sai Kuma an sallami mutane 16 da cikin mutane 238 wadanda ke jiran shariya.
Har wayau mutane 24 suna jiran hukuncin kisa a yayinda mutane 5 Kuma na jiran hukuncin zaman gidan yari na Rai da Rai.
Kawo yanzu daidan yarin na dauke da fursunoni 440 Mai makon 500 da aka kaiyade a gidan yarin.
Da taketiwa wadanda aka sallama jawabi shugabar Alkalain jahar Adamawa Maisharya Hafsat Abdulrahman ta baiyana cewa an sallamesune saboda laifukasu basu taka Kara sun karyaba Wanda hakan yasa kwamitin ya duba Kuma yayi la akari tare da tausayawa yanke shawaran sallamarsu.
Ta kirayesu da su maida hankali wajen nuna halaye na gari da Kuma yin abinda zai taimaki rayuwarsu.
Tunda farko a jawabinsa shugaban gidan yarin Yola H. T Ibrahim ya yabawa shugabar Alkalain da tawaganta bisa wannan kokari da sukayi na ziyartan gidajen yari.
Yace Yana Mai fatan wannan ziyaran zai taimaka wajen sanya farin ciki ga wasu mazauna gidajen yari. Ibrahim ya shawarci wadanda suka samu yancinsu da sukasance jakadu na gari a tsakanin Al umma bayan sun bar gidan yari.
Comments
Post a Comment