Rundunan tsaro Civil Defence ta lashi takwabin baiwa Al umma kariya a lokacin zanga zanga kasa da za ayi a jahar Adamawa.
A kokarinta na ganin an samu zaman lafiya a yunkurin da gamaiyar kungiyar dalube ta kasa wato NANS keyi na gudanar da zanga zangan lumana. Rundunan tsaron bada kariya ga farin hula wato Civil Defence ta gudanar da taro na musamman da kungiyar dalube dake Jami o I a fadin jahar dama sauran masu ruwa da tsaki domin tattaunawa ganin ba a samu matsalaba a yayin zanga zanga.
Taron Wanda ya samu halartan sarakunan gargajiya, kungiyoyin addinai, dama kungiyoyin fararen hula harma Dana dalube daban daban domin tattauna illar da zanga zangan zai iya haifarwa a tsakanin Al umma.
Taron Wanda ya gudana karkashin jagoranci kwamandan Rundunan a jahar Adamawa Idris Bande ya ja hankalin dalube da kada sukasance masu karya doka a lokacin zanga zanga, duk da cewa doka ya basu damar yin zanga zangan lumana to Amma doka bai basu damar tayar da fitina ko yin tarzomaba.
A zantawarsa da manema labarai kakakin rundunan tsaro ta Civil Defence a jahar Adamawa DSC Nyako Amidu Baba yace baya ga taron da aka gudanar Kwamandan ya bada umurnin girke Jami an tsaron na Civil Defence domin baiwa Al umma kariya.
Rundunan tana Mai shawartan Al umma musammanma matasa da su nisanta kansu daga shiga dukkanin abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin Jama a.
A cewar kakakin rundunan tsaron Civil Defence rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin Al umma don haka ya kamata su kasance suna baiwa rundunan hadin Kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran gudanar da aiyukanta na baiwa jama a kariya.
Comments
Post a Comment