Rundunan tsaron Civil Defence ta lashi takwabin dakile aikata laifuka a fadin jahar Adamawa.

 





A kokarinta na dakile aiyukan ta addanci, sace sace, dama sauran aikata laufuka. Rundunan tsaro bada kariya ga farin hula wato Civil Defence dake jahar Adamawa ta gargadi duk Mai aniyar aikata laifuka da ya nisanta kansa da aikata laifuka domin kaucewa fushin rundunan.




Kwamandan Rundunan a jahar Adamawa ID Bande ne ya bada wannan gargadi a lokacinda yake ganatarwa manema labarai mutane 12 da ake zargi da aikata laifuka a shelkwatar rundunan dake sakatariyar tarayya a Yola.




Kwamandan a wata sanarwa da kakakin rundunan ta Civil Defence a jahar Adamawa DSC Amidu Nyako ya fitar ya baiyana  karara cewa rundunan bazata bari ta na gani ana aikata laifuka ba saboda haka a kaucewa duk wasu aikata laifuka.




Kwamandan Bande yace karkashin shugabancinsa bazai yarda wasu suna sace saceba saboda haka duk masu gudanar da irin wannan aiyuka to su tuba domin rundunan baza ta lamunce da aikata laifuka ba. Domin a cewarsa jahar Adamawa babu maboyar masu aikata laifuka domin rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin Al umma.



Ya Kuma baiyana godiyarsa da Jin dadinsa ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri dangane da daukan matakan tsaro da yayi a fadin jahar Adamawa tare da tabbatarwa Al umma cewa duk Wanda aka samu Yana yiwa doka Karan tsaye to zai fuskanci hukunci.




Yace wannan umurnin ne daga Babban Kwamandan Rundunan na kasa Dr Ahmed Abubakar Audi inda ya bukaci dukkanin jihohi da sanya ido tare da kare kayakin gwamnati Dana jama a.




Harwayau Kwamanda Bande ya kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance suna sanya idon akan kayakin gwamnati dake yankunansu da Kuma Kai rahoton dukkanin abinda basu yarda da Shiba ko mutuminda ke kokarin barnata kayakin gwamnati zuwa ofishin rundunan ta NSCDC dake kusa.



Rundunan a shirye take ta cigaba da ganin an samu zaman lafiya dama kare kayakin Al umma harma da dakile aiyukan ta addanci a fadin jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE