Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani danbanga bisa zarginsa da yin sojan gona.

 





Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran cika hanu da wani danbanga da ake zargin da yin sojan gona inda yake ikirarin cewa shi Jami in dan sanda harma Yana damfaran mutane musammanma matuka keken Napep.




Wanda ake zargin Mai Suna Shafi u Abdulkadir Mai shekaru 27 mazaunin anguwar Yelwa ne dake cikin garin Jimeta a karamar hukumar yola ta arewa a jahar Adamawa.




Kakakin rundunan yan sandan dake jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Sanarwan tace an samu nasaran kama Wanda ake zargin biyo bayan wasu bayanain sirri da da wasu Yan Sakai suka samu dangane da aiyukansu na cutar jama a inda aka sameshi sanye da kakin Yan sanda.




Sanarwan ta Kara da cewa da zaran an kammala bincike kan Wanda ake zargi za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci shariya.




Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu Kai rahoton duk wani batagari ga rundunan akan lokaci domin ganin an samu nasaran kare lafiyar Al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE