Zaman lafiya: An gudanar da bikin ranan zaman lafiya ta duniyar a jahar Adamawa.

 





A cigaba da bikin ranan wanzar da zaman lafiya ta duniyar Rundunan tsaro bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence shiyar jahar Adamawa tare da hadin gwiwar kungiyar Search for Common Ground sun samu nasaran gudanar da bikin cikin na ahekar 2024 cikin lumana a fadin jahar Adamawa.




Bikin Mai taken wanzar da Al adar zaman lafiya tare da gudanar da tattakin lumana tare Kuma da gabatar da jawabai daban daban a dakin taron gidan gwamnati da kenan Yola.




Hakan na kushena a cikin wata sanarwa da kakakin rundunan Civil Defence a jahar Adamawa DSC Amidu Nyako Baba ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Da yake gabatar da jawabinsa Kwamandan Rundunan ta Civil Defence  a jahar Adamawa Idris Bande ya baiyana irin muhimmanci da ranan zaman lafiya ta duniyar ke dashi don haka rundunan zatayi dukkanin abinda suka dace domin bunkasa zaman lafiya.




Yace rundunan hakkintane da dakile duk wata fitina musammanma masu hakan muadinai ba bisa Ka idaba harma da dakile rikici a tsakanin manoma da makiyaya a fadin jaha.



Kwamandan ya Kara da cewa a dokan rundunan ta NSCDC sashi na 3 no na Daya ya baiwa rundunan karfi kwantar da duk wata fitina a tsakanin Al umma da Kuma warware duk wata fitina domin samun cigaban zaman lafiya.




Harwayau Kwamanda ya yabawa gwamnatin jahar Adamawa wajen Samar da yanayi Mai kyau da Kuma wanzar da zaman lafiya.



Kwamandan Idris Bande ya yabawa kungiyar ta Search for Common Ground bisa gudumawa da take nayarwa wajen wanzar da zaman lafiya tare da aiki tukuru Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen Samar da nasaran aiyukansu.




Shima a jawabinsa bako Mai jawabi wato John  Ngamsa ya Yana da matukan muhimmanci kowa ya bada nashi gudumawa wajen wanzar da zaman lafiya saboda kowa Yana da damar da zaiyi duk abinda zai kawo zaman lafiya a tsakanin Al umma.



Taron dai ya samu halartan Jama a daban daban, masu ruwa da tsaki, kungiyoyi, sarakunan gargajiya, kungiyoyi fararen hula da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE