Gwamnatin jahar Adamawa ta ragewa matasa da mata radadin

 






Gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ta taka rawan gani wajen rage radadin talauci dama rashin aikinyi a tsakanin matasa da mata a fadin jahar Adamawa.




Kwamishinan koyar da sana o I a jahar Adamawa Hammanjuba Gatugal ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.





Hon. Hammanjuba yace tunda  gwamna ya kirkiro ma aikatar, ma aikatar ta horar da matasa da mata sana o I daban daban da suka hada da kafinta, walda, aikin tela da dai sauransu.




Kwamishinan yace ko a kwanan nan ma gwamnan ya rabawa mata kude dubu hamsin hamsin kowannensu domin su gudanar da sana o in dogaro da Kai domin ganin a Samar da aiyukan Yi a tsakanin Jama a, musammanma matasa da mata.



A cewarsa gwamna ya gudanar da aiyukan cigaba da suka hada da hanyoyin, kiwon lafiya, tsaro, Ilimi, harkokin noma, kiwo da dai sauransu hakan nema yasa aka samu wanzuwar zaman lafiya a fadin jahar baki Daya.




Kwamishinan ya Kuma kirayi matasa da mata musammanma wadanda suka samu kayakin sana o I da suyi amfani da kayakin da Kuma illimi da suka samu domin hakan zaitaimaka wajen bunkasa tattakin Arziki da cigaba.




Da wannan nema kwamishinan yake kira ga gwamna da ya Samar da wasu kwamitin da zai rinka bibiyan wadanda aka basu kayakin yin sana ar bayan an basu horo domin tabbatar da ganin basu sayarba. Domin a cewarsa Babban kalubalen da ake fuskanta shine wasu inadan an basu kayakin sai su sayar.




Hammajumba ya kirayi dau kacin Al ummar jahar ta Adamawa da sukasance suna baiwa gwamna Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar.





Ya Kuma baiyana fatarsa ga gwamna Ahmadu Fintiri tare dayi masa adu ar Allah ma daukakin sarki ya Kara masa lafiya ya taimakeshi ya Kuma kammala mulkinsa lafiya ba tare da matsaloliba.



Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.