Rundunan Yan sanda a jahar Adamawa ta fara gudanar da bincike kan zargi Yan Banga da cin zarafin wani a kasuwar shanu dake Song.
Rundunan yan sanda jahar Adamawa ta fara binciken dangane da tsare wani da akayi a kasuwar shanu dake cikin karamar hukumar Song a jahar Adamawa ba bisa Ka ida ba Wanda ake zargin Yan Banga da aikatawa Wanda ya karade shafukan sada zumunta.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya tabbatar da cewa rundunan bazatayi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da bincike domin rundunan baza ta lamunce da laifukan cinhanci da rashawaba ko cin zarafiba.
Kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Kwamishinan Yan sanda yace domin ganin an samu zaman lafiya a tsakanin Al umma a jahar Adamawa ne yasa runduna ta kudiri aniyar Saka kafar wando Daya da duk maiyiwa zaman lafiya barazana ko Kuma yiwa doka Karan tsaye.
Da wannan nema rundunan take shawartan jama a musammanma wadanda aka musu ba daidaiba da su kawo rahoton domin gudanar da bincike dangane da lamarin.
Sanarwan ta Kuma shawarci daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu baiwa rundunan hadin Kai domin ganin ta samu nasaran gudanar da binciken domin ganin an gudanar da adalci dama Samar da zaman lafiya.
Comments
Post a Comment